14 Maris 2021 - 14:01
Covid 19 : Ministan Lafiya A Jordan Ya Yi Murabus

Ministan lafiya na Jordan ya yi murabus bayan mutuwar wasu majinyatan cutar korona a asibiti sakamakon karancin iskar oxygen.

ABNA24 : Nathir Obeidat, ya sanar da yin murabus ne sakamakon mutuwar majinyatan a wata asibiti kusa da babban birnin kasar Amman.

Kafofin watsa labaran kasar sun ce mutum shida suka mutu, lamarin da ya fusata al’umma a Jordan.

Firayi ministan kasar ya ba da umarnin gudanar da binciken gaggawa kan lamarin.

342/